Shugabannin Kasashen Afirka Na Taro Kan Rikicin Ivory Coast

Yadda sabanin ra'ayin bangarorin siyasa ke jawo yamutsi a Ivory Coast kenan.

Wata tawaggar shugabannin kasashen Afrika tace tana fatar nan da zuwa makon gob eta iya warware rikicin dake addabar kasar Cote d’Ivoire, inda ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin manyan ‘yan siyasar kasar biyu: shugaba Laurent Gabgbo da abokin adawarsa Alassane Ouattara.

A yau ne aka shirya cewa shugabannin kasashen Burkina Faso, Chad, Mauritania, Afrika ta Kudu da Tanzania zasu hadu a Nouakchott, babban birnin kasar Mauritania don neman war ware wannan rikicin. Daga baya kuma ake sa ran zasu tashi daga nan, su tare a Abidjan ta Ivory Coast din.

Daman dai wadannan shugabannin duk suna cikin wani kwamitin musamman da aka kafa, wanda aka baiwa aikin maido wa ivory Coast zaman lafiya na siyasa.

A wata hira da yayi da nan VOA ne, kakakin kungiyar ECOWAS, Sony Ugoh yace shugabannin na fatar kafin makon gobe sun sami tabattacciyar hanyar sulhunta rikicin.

Wannan tana faruwa ne kwana daya bayanda sojojin dake biyayya ga hinjararren shugabankasar ta Cote d’Ivoire Laurent Gabgbo suka hallaka wasu mata bakwai ta hanyar bindige su yayinda matan ke zajnga-zangar lumana ta neman shugaban ya sauka daga kan karagar mulki.