Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Fuskantar Karancin Man Fetur a Ivory Coast, An Kuma Rufe Wasu Gidajen Jaridu


Wasu 'yan gudun hijiran rikicin Ivory Coast kenan dauke da 'yan kayakinsu.
Wasu 'yan gudun hijiran rikicin Ivory Coast kenan dauke da 'yan kayakinsu.

Jama’a a Ivory Coast suna fama da rikicin siyasar kasar, inda aka fara fuskantar karancin man fetur da kuma rufe gidajen jarida takwas.

Jama’a a Ivory Coast suna fama da rikicin siyasar kasar, inda aka fara fuskantar karancin man fetur da kuma rufe gidajen jarida takwas.

Masu kamfanonin jaridun masu zaman kansu sun fito da bayanai na hadin gwiwa a yau Talata inda su ka yi nuni da yadda magoya bayan shugaban da ke kan gado Laurent Gbagbo ke ta amfani da bangaren doka da ‘yan sanda wajen gallaza masu. Kamfanonin jaridan sun ce an auna su ne saboda kawai sun ki su goyi bayan Mr. Gbagbo.

Shugaban ya yi biris da matsin lambar al’ummomin duniya na bukatar ya sauka ya kuma mika ragamar iko ga Alassane Ouattara, wanda akasarin kasashe su ka ayyana a matsayin wanda ya ci zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamba.

A wata sanarwa a yau Talata, kungiyar rajin kare ‘yancin ‘yan jarida mai suna Reporters Without Borders a turance ta ce ana gallazawa tare da yi wa kamfanonin jarida masu zaman kansu barazana. Kungiyar ta kuma ce an fara yakin kafafen yada labarai tsakanin magoya bayan Gbagbo da magoya bayan Ouattara, wanda hakan ya haifar da yana mara kyau ga ‘yan jarida.

Kungiyar ta ce wasu mutane dauke da kulake da adduna sun hallaka wani ma’aikacin kamfanin jaridar da ke goyon bayan Gbagbo a Kudancin Abidjan ranar Litini.

XS
SM
MD
LG