Shugaban Amurka Barack Obama ya gana a kebe tare da shugabar kasar Faransa Nicolas Sarkozy da shugabar kasar Jamus Angela Merkel, wadanda ke zama a sahun gaban kasashen turai da tattalin arziknsu keda karfi.Anyi tattaunawar ce a taron kolin G-20 da aka fara Alahmis. Shugaba Obama yace tarayyar Turai na daukan kwararan matakai domin maganta matsin lambar yawan bashin dake kan Amurka, kuma yace akwai fatan taron kolin kasashe masu arzikin da ake yi yanzu zai taimaka da muhimman shawarwarin kaiwa ga warware matsalolin tattalin arzikin kasa da kasa baki daya.