Shugabannin Jam'iyyar LP Na Jihohi Sun Nuna Goyon Baya Ga Abure

Shugaban jam'iyyar LP, Julius Abure

Shugaban jam'iyyar LP, Julius Abure

Tun da farko, wadanda suka samu umurnin kotu na dakatar da Abure sun yi dafifi a helkwatar jam’iyyar don hana shi yin jagaoranci.

Shugabannin jam'iyyar adawa ta Labor Party (LP) na jihohin Najeeriya, sun mara baya ga shugaban jam'iyyar Julius Abure da umurnin kotu ya dakatar.

Hakan ya janyo dambarwa a tsakanin bangarorin biyu har sai da kungiyar kwadago ta fitar da matsaya.

Tun da farko, wadanda su ka samu umurnin kotu na dakatar da Abure sun yi dafifi a helkwatar jam’iyyar don hana shi yin jagaoranci.

Shugabannin jihohin sun ce wadanda su ke adawa da Abure na halin dakatarwa ne kafin su dau matakin don haka ba su da hurumin hakan.

A sanarwa daga shugaban kungiyar kwadago NLC Komred Joe Ajero da ke mallakar jam’iyyar ta LP, kungiyar ta ce Abure ta sani a matsayin shugaba.

Jami’in kungiyar Komred Nasir Kabir ya yi karin bayani, ya na mai cewa tuni kungiyar ta dau matakan shawo kan wadanda ya ayana da ‘yan kutse.

Don haka shugabannin na jihohi sun zargi masu adawa da Abure da neman dakatar da yunkurin jam’iyyar ta LP na kalubalantar sakamakon zaben 2023 ne.

Kakakin kamfen din dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi, wato Yunusa Tanko ya karfafa cewa an sa Abure a gaba ne don dakile karar jam’iyyar a kotu.

Shugabannin sun kara da cewa ya dace kowa ya jira sai an kammla babbar shari'a kafin kawo kowane korafi.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Shugabannin Jam'iyyar LP Na Jihohi Sun Nuna Goyon Baya Ga Abure - 2'36"