Shugabannin Isra’ila da na Falasdinawa sun fara tattaunawa kan wasu muhimman matsaloli da dama da su ka raba kawunan bangarorin biyu a lokacin tattaunawa ta kai tsaye a Masar, to amman tattaunawar ta jiya Talata ba ta samar da wani cigaba na a-zo-a-gani ba game da tankiyar da ake yi kan gine-ginen matsugunan Yahudawa a yankuna da Isra'ilar ta mamaye.
Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Natanyahu da Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas sun sake wata zama ta ba-zata da Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton jiya Talata, to amman babu wani labarin cigaba sosai.
Wakilin Amurka a Gabas ta Tsakiya, George Mitchel, ya gaya wa manema labarai cewa Shugabannin Isira’ila da Falasdinawa sun yi tattaunawa muhimmiya kuma mai zurfi game da muhimman batututuwa, ciki har da batun jadawalin sabuwar kasar Falasdinu, tabbacin tsaron kasar Isra’ila, da matsayin birnin Qudus a siyasance da kuma makomar ‘yan gudun hijira Falasdinawa.
Ya ce tattaunawar na gudana yadda ya kamata, to amman bai yi bayanin ko an sami wani cigaba ba game da batun matsugunan Yahudawan. Za a cigaba da tattaunawar yau Laraba a birnin Qudus.