Shugabannin ECOWAS Sun Yi Allah Wadai Da Juyin Mulkin Mali

Shugabanin kasashen yammacin Afrika mambobin kungiyar CEDEAO sun kara yin Allah wadai da juyin mulkin da ya kifar da shugaba Ibrahim Boubacar Keita daga karagar Mulki

A karshen taron da suka gudanar ta bidiyo a jiya alhamis shugabanin kasashen Afrika ta yamma sun yi Allah wadai da abinda suka kira yunkurin kifarda zababbiyar gwamnatin dimokradiya da Ibrahim Boubakar keita ke jagoranta saboda haka suka umurci sojoji su canza tunani. Suna masu cewa ba su da kowane irin halaccin shugabanci.

A cikin jawabinsa, Shugaban rikon kungiyar ECOWAS Issouhou Mahamadou na Nijer ya bayyana cewa, “muna bukata sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Mali su gagauta sakin shugaba Ibrahim Boubakar Keita da dukkan jami’an da aka kama” Kungiyar ta CEDEAO ta bukaci sojoji su mayarda hambararen shugaban akan kujerar shugabancin kasar ta Mali.

Taron na kungiyar ECOWAS ya yanke shawarar dakatar da dukan wata zirga zirga tsakanin kasar Mali da makwaftanta ba shiga ba fita in ban da kayan cimaka da magunguna da man fetur da wutar lantarki sannan ta bukaci abokan hulda su bi sahu tare da kakaba takunkumi ga sojojin da suka yi wannan juyin mulki kafin isar rundunar hadin guiwar da kasashen na CEDEAO ke shirin aikawa zuwa kasar Mali.

Shugabannin juyin mulkin Mali

Taron na jiya alhamis yace zai aika wata tawaga domin ganawa da sojojin da suka tunbuke shugaba Ibrahim Boubakar Keita don sanar da su cewa lokacin hambarar da mulki ya wuce.

Yanzu dai ana iya cewa kallo ya koma sama domin a fili take wadanan matakai da ECOWAS ta dauka wani al’amari ne da ake ganin zai kara tabarbarar da dangantaka a tsakanin al’umar Mali da wannan kungiya wace tun dama suke yiwa kallon kungiyar kare hakkin shugabanin kasashen Afrika ta yamma.

Ku saurari cikakken rahoton Souley Mummuni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Shugabannin CEDEAO Sun Yi Allah Wadai Da Juyin Mulkin Mali:3:00"