Sauya matsayi kan cire darussan addinin Musulunci da na Kirista a manhajar makaratun Najeriya, ya jawo jin dadi ga shugabanin addinan kasar.
Tun farko dai ma’aikatar ilimin kasar ta kirkiro da wani darasi ne na wayar da kan ‘yan kasa da ya lakume karatun addini suka zama kananan darussa a cikin babban darasi, dama anyi hakan ne da tunanin kowane dalibi zai tsinci wani shashe na ilimin addinin dan uwansa.
Imam Inuwa Muhammad, maitaimakin daraktan tsare tsare na ma’aikatar ilimi, yace Allah ya kawo mu lokacin na Gwamnati mai sauraran koke koken jama’a, yanzu wanda yake dan Kirista yaje ya karanta Kiristanci idan dan Musulmi ne yaje ya karanta Musulunci, dama hanyar da gwamnati ke nema a gane yadda za a zauna da juna saboda a samu ci gaba a fanin ilimin kasar.
Gabanin wannan sauyin korafen ya fito daga kungiyar Kiristoci ta Najeriya, (CAN) dake ganin ana son a soke ilimin addini Kirista ne na CRK, tunda a tsarin kananan darussan akwai koyon Larabci da Faransanci.
Rev. Musa Asaki sakataren kungiyar Kiristocin Najeriya, ya ce da farko an dama masu lissafi a manhajar karatun daliban inda akayi wasu sauye sauye amma a yanzu sunyi na’am da wannan sabon mataki na maido da mahajar addini a makarantu.
Da alamu wannan mataki zai kwantar da kurar mahauwara kan ilimin addini a makarantun gwamnatin Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5