Yayin da ‘yan kasar Venezuela ke shirin shiga yajin aikin yau laraba , shugaban kungiyar kasashen yankin da ake cewa OAS a takaice sun gana jiya talata da tsohon mai gabatar da kara na kotun manyan laifuka na kasa da kasa akan yiwuwar a tuhumi mahukuntar kasar ta Venezuela akan take hakkin bil-adama.
Sakataren na kungiyar OAS Janar Luis Almagro ya fada a wajen taron manema labarai a jiya talata cewa lauya Luis Moreno-Ocampo zai taimaki kungiyar ya gani ko mahukuntar kasar ta Venezuela sun aikata ayyukan assha musammam akan abinda keda nasaba da cin zarafin bil adama wanda ya cancanci kotu ta kasa da kasa ICC ta gudanar da bincike akan sa.
Moreno Ocampo yace za a ji baasi daga sassan biyu, daga wanda ake tuhummar an take hakkin su da kuma bangaren gwamnatin ta Venezuela
Facebook Forum