Hukumomi a kasar Burkina Faso sun nada tsohon Ministan harkokin wajen kasar Michel Kafando a matsayin shugaban kasa na wucin gadi, kuma an dora masa alhakin jagorancin kafa gwamnatin farar hula.
WASHINGTON, DC —
Kwamitin daya kunshi yan siyasa da sojoji da shugabanin addinai dana kungiyoyin jama'a ne ya bada sanarwa zaban Mr Kafando a yau litinin kwana daya bayan an fara yin shawarwari nada shugaban.
Shugaban masu hamaiya Zephirin Diabre ya baiyana zaban Mr Kafando a zaman na yi da wajewa.
Mataki na gaba shine Mr Kafando zai nada Prime Minista wanda shi kuma zai kafa gwamnatin wucin gadi.
A yayinda yake zantawa da yan jarida a yau Litinin sabon shugaban yace gwamnatinsa zata yi aikin samun nasarar kafa gwamnatin farar hula.