Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burkina Faso ta Samu Shugaba na Wucin Gadi


Issac Yacouba Zida shugaban soja da ya karbi mulki watan jiya.
Issac Yacouba Zida shugaban soja da ya karbi mulki watan jiya.

A wani yunkurin kaucewa takunkumi sojojin Burkina Faso sun nada shugaban wucin gadi farar hula

Shugabannin mulkin soji na Burkina Faso sun bayyana Michel Kafando, wani farar hula a matsayin shugaban kasar farar hula na wuccin gadi kamar yadda kungiyar Afirka ta bukata.

'Yan siyasa da wakilan sojoji, da kugiyoyi masu zaman kansu da shugabannin addinai da na al'ummai sun gana jiya Lahadi don nada sabon Shugaban wuccin gadin kasar. Sabon shugaban zai jagoranci shirin mayar da kasar kan mulkin dimokradiya bayan dadadden Shugaban kasar Blaise Compaore wanda ya sauka a watan jiya babu shiri.

An sa ran samun Shugaban wuccin gadin tun da daren jiya Lahadi kafin a tabbatar da shi yau. Za’a kuma nada Firayim Minista nan da zuwa ranar Laraba.

Alatilas Mr. Compaore ya ajiye aiki ranar 31 ga watan Oktoba sabili da kalubalantar da ya fuskanta daga ‘yan adawa da matasan kasar. Yukurin da yayi na canza kundun tsarin mulkin kasar ta yadda zai iya sake tsayawa takarar Shugaban kasa don ya tsawaita mulkinsa na tsawon shekaru 27 ya kawo masa cikas.

An maye gurbinsa da Laftana Kanar Isaac Yacouba Zida, bayan da sojoji su ka jingine kundin tsarin mulkin kasar.

A farkon wannan watan, Kungiyar Tarayyar Afirka ta bai wa Shugabannin mulkin sojin Burkina Faso wa'adin mako biyu su kafa mulkin wuccin gadi, tare da nada Shugaban kasa farar hula na wuccin gadi. Wa’adin zai kare yau. Da sun ki da kungiyar ta kakabawa kasar takunkumi.

XS
SM
MD
LG