Shugaban Sashen Whatsapp Na Shirin Yin Murabus

Shugaban sashen sakon gaggawa na Whatsapp, daya daga cikin bangarori na kamfanin Facebook Mr. Jan Koum, zai ajiye aiki biyo bayan rashin jituwa da suka samu da manyan kamfanin, na tsarin da akebi wajen ajiye bayanan mutane.

Mr. Jan, ya rubuta a shafin shi na facebook yana cewar “Kusan shekaru goma kenan da muka fara wannan kamfanin, wanda muka kirkiri manhajar wazob, kuma mun samu gaggarumar nasar, wanda muka hada gwiwa da wasu mutane masu haza, don haka lokaci yayi da nima ya kamata na nemi wani abun yi”

Duk dai da cewar bai sanar da ranar da zai bar kamfanin ba ya zuwa yanzu, jaridar Washington post ta wallafa cewar shugaban zai bar kamfanin ne, biyo bayan rashin jituwa da ya abku a tsakanin shi da wasu masu jan ragamar babban kamfanin na facebook.

Wanda suka nemi amfani da bayanan mutane ta hanyar da bai kamata ba, kana da rage karbin tsarin tsaro na manhajar ta wazob, wanda bai aminta da matakin ba.

A tabakin wasu na kusa da shi, sun bayyanar da cewar, tsarin shi na shugabanci ya banbanta da na wasu daga cikin tsarin yadda wasu shugabannin ke neman a tafiyar da kamfanin.