Shugaba Duterte, wanda ya nemi majalisar dattawan kasar ta tsawaita wa’adin da suka bashi na yaki da masu mu’amulla da muggan kwayoyi, ya ce sukar da masu kare hakkin bil’adama ke yi, ba zai hana shi ci gaba da yakar masu shan muggan kwayoyin ba.
“Hitler ya kashe yahudawa miliyan uku, muna da masu shan muggan kwayoyi miliyan uku, zan yi farin ciki idan na kashe su.” Shugaba Duterte ya ce a birnin Davao bayan wata ziyara da ya kai Vietnam.
A lokacin jawabin, shugaban na Philippines, ya yi biris da Amurka da kasashen Turai, inda ya ce in sun ga dama su kirashi duk abinda su ke so.
A watan Yunin wannan shekarar nan, shugaba Duterte ya dare karagar mulkin kasar, bayan da ya lashe zaben a watan Mayu, ya kuma sha alwashin sai ya ga bayan matsalar cin hanci da rashawa da masu safarar muggan kwayoyi a kasar ta Philippines mai yawan jama’a miliyan 100.