Shugaban Nijeriya ya ziyarci birnin Kano da tashin hankali ya daidaita

  • Ibrahim Garba

Wasu daga cikin gawarwakin mutanen da su ka mutu

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya ziyarci jihar Kano ta arewacin Nijeriya

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya ziyarci jihar Kano ta arewacin Nijeriya a jiya Lahadi a sa’ilinda adadin wadanda su ka mutu a hare-haren da ‘yan Boko Haram su ka kai ranar Jumma’a ke ta karuwa.

Kimanin mutane 170 sun mutu a halin yanzu, kuma yawancinsu ‘yan sanda ne da soji, a yayin da aka yi ta jefa bama-bamai da harbe-harbe kan ofisoshin ‘yan sanda da gine-ginen gwamnati a birni na biyu a girma a Nijeriya.

Wannan harin da Boko Haram ta dauki alhakin kaiwa, an bayyana shi da cewa shi ne ya fi muni.

Shugaba Jonathan, wanda Kirista ne, ya gana da Sarkin Kano, inda ya sha alwashin daukar mataki kan wadanda ya bayyana da cewa ‘yan ta’adda ne.

Kungiyar ta ce niyyarta ita ce kakama tsattsaurar tsarin shari’ar Musulunci a fadin kasar. Wani mai magana da yawun ‘yan Boko Haram ya fadi ran Jumma’a cewa harin martani ne na kama wasu ‘yan kungiyar da dama da aka yi a birnin na Kano.

Sojoji sun yi ta sintiri a jiya Lahadi a wannan birni na arewacin Nijeriya don tabbatar da tsaro da kuma gamsar da mazauna birnin cewa wannan tashin hankalin ba zai sake faruwa ba.

To amman a jihar Bauchi da ke makwabtaka da Kano, wani harin da aka kai da asuba ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 10. An kuma kai hari kai majami’u biyu.

Aika Sharhinka