Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria ya lashi takobin cewa gwamnatinsa zata dauki dukkan matakan daya kamata domin farauto yan ta'adar da suka kai hari baban Masalacin Kano, suka kashe fiye da mutane tamanin da raunana akalla mutane dari.
Yau Asabar shugaba Jonathan ya gabatar da wata sanarwa yana kira ga 'yan Nigeria da kada su karaya.
Jiya Juma'a bayan an fara sallar juma'a bama bama suka tashi sa'anan kuma harbe harbe suka biyo bayan tashin bama baman a baban Masalacin birnin Kano a arewacin Nigeria.
Shedun gani da ido sunce sun ga mutane da dama wadanda suka ji rauni, suka kuma baiyana tsoron cewa kila akwai wadanda suka mutu bayan da bama bamai guda biyu suka tashi kusa da baban Masalacin Juma'a ta Kano.
'Yan sanda sun isa wurin suka tinkari matasan da suka fusata.
Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta yi Allah wadai da da harin. Mai magana da ywun baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya yace Mr. Ban Ki-moon yayi kira ga hukumomin Nigeria da su yi saurin kamo wadanda suka aikata wannan danyen aikin domin a hukunta su.
Babu kungiyar data yi ikiratin cewa ita keda alhakin ki harin, to amma tana yiwuwa ayi zaton kungiyar Boko Haram ce ta kai harin, wadda a baya ta kai hare hare makaanci wannan a birnin na Kano