Shugaban yana son a janye duk wasu shingayen binciken ababen hawa a kan hanyoyin kasar.
To masu ruwa da tsaki sun soma bayyana ra'ayoyinsu. Kwamred Sulaiman Adamu Dan Zaki shugaban kungiyar ma'aikatan sufurin Najeriya yace akwai lokacin da suka yi koke-koke game da take-taken da ake yi a hanya. Yace idan mutum ya dauko shanu daga Maiduguri ya zo hanya a tsayar dashi a ce ya saukesu ba karamar wahala aka jawo mashi ba.
Yace direba zai dauki kudi nera dubu dari biyu daga Maiduguri zuwa Legas, idan ba sa'a aka yi ba kudin ba zasu kai ba saboda jami'an tsaro akan hanya dake neman na goro. Saboda haka kawar da shigayen zai ragewa mutane tsadar abinci. Domin duk wani abun da aka kashe akan hanya karshenta akan talaka yake dawowa.
Su ma kungiyoyin fararen hula sun sha yin korafi can baya akan yadda ake kutuntawa jama'a da shingayen sojoji da 'yansanda. Kwamred I.G. Wala yace shingayen sun dade ana korafe-korafe a kansu. Shigayen sun zama wuraren azaba da fitina da kashe kudi ga duk wanda yake tafiya da abun hawa akan hanya. Sai ka bada wani abu zaka wuce. Idan baka bayar ba ba zaka wuce ba. Duk yawan shingayen basu hana bamabamai tashi ba.
Shugabannin sojoji da na 'yansanda sun yi anfani da shingayen sun yi kudi. Miliyoyi suke karba da sunan biyan sojoj da 'yansandan dake kan hanyoyi amma yawancinsu basa samn kudin.
Wasu suka ce abun da shugaban kasa yayi ya faranta masu ciki saboda irin azabar da suka sha a hannun sojojin dake kafa shinge a hanya. Wasu sojojin duka suke yiwa mutane su jefa mutum cikin laka tare da wulakantashi da kuma yin kwace. Ban da haka sojoji na kawo cikas akan tafiyar ababen hawa. Wani lokacin sai su tsare hanya su hana mutane wucewa na sa'o'i da dama.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5