Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya ki amincewa da karin wa'adi ga shugabannin jam'iyyarsa ta APC mai mulki bayan wa'adinsu.
Tun farko an amince a kara masu wa'adin shekara daya saboda wa'adinsu zai kare ne a watan Yuni mai zuwa.
Yayinda shugaban ke magana a taron majalisar kolin jam'iyyar ya ce tsarin mulkin jam'iyyar ya yi tanadin duk wanda yake rike da mukami kuma ya na son ya sake tsayawa zabe sai ya bar mukaminsa wata daya kafin zaben.
Shugaba Buhari ya nuna fargaba matuka aka kaucewa tsarin mulkin jam'iyyar saboda duk wani zabe da 'yan rikon kwarya ko wadanda aka karawa wa'adi suka shirya ba zai samu karbuwa ba a doka. Wannan matsayin shugaba Buhari ya kara zaman zullumi a hedkwatar jam'iyyar, da kuma yiwuwar kawar da shugaban jam'iyyar dake kan gado Mr. John Odigi Oyegun wanda baya jituwa da uban jam'iyyar Bola Tinubu.
Yusuf Sallau Mutun Biyu lauya ne mai zaman kansa a Abuja kuma ya yi sharhi akan lamarin. Ya ce kamar dokar kasa dokar APC ma ta ba shugabanninta wa'adin mulki na shekaru hudu. Duk wanda yake son ya sake zama shugaba sai ya sauka wata daya kafin zabe.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5