Shugaban sojojin kasa na Najeriya Janar Yusuf Tukur Buratai ya tabbatar cewar gwamnatin tarayya ta amince da kafa bataliyan na soja a yankin Birnin Gwari cikin jihar Kaduna.
Manufar kafa bataliyar ita ce shawo kan yawan fashi da makami tare da sace mutane da kisa tsakanin Kaduna da Birnin Gwari da kuma tsakanin Abuja da Birnin Gwarin dake faruwa kusan kullum. Gwamnati na son tabbatar da cewa an yaki ta'addancin dake yiwa yankin barazana da ma kasar gaba daya.
Bayan ya gana da shugaba Buhari, Janar Buratai ya yiwa manema labarai karin bayani akan kafa bataliyan sojoji din a yankin Birnin Gwari da ayyukan da ake kyautata zaton zata yi.
A cewar Janar Buratai umurni ne da shugaban Najeriya ya bayar domin kawar da miyagun mutane a dajin dake kewaye da yankin da kuma hanyoyin da suka nufi Kaduna da Abuja. Janar Buratai ya ce tun shekaru biyu da suka wuce aka ba da shawarar samar da sojoji a yankin.
Janar Buratai ya ce ya tafi yankin ya ga inda za'a kafa bataliyar, kuma tuni an fara aikin sintiri da bada tsaro a yankin tare da hadin gwuiwar sauran jami'an tsaron kasar.
Ga Umar Faruk Musa da karin bayani a wannan rahoton
Your browser doesn’t support HTML5