Bayan musayar zafafan kalamai a makon da ya gabata, kan shirin gina katanka a kan iyakar Amurka da Mekziko (Mexico), Shugaban kasar Mekziko Enrique Pena Nieto ya soke shirin kai ziyara Fadar Shugaban Amurka ta White House, a cewar wani rahoton da jaridar Washington Post ta rubuta jiya Asabar.
Pena Nieto da Trump sun yi magana ranar Talata, inda su ka shafe lokaci mai yawa kan batun gina katangar a tsawon sa’a guda da su ka yi, a cewar majiyar da ta yi bayani ma jaridar ta Post.
Yayin da ya ke yakin neman zaben Shugaban kasa, Trump ya yi alkawarin cewa zai gina Katanga akan iyakar Amurka da Mexico don rage kwararowar bakin haure. Ya kuma gaya ma magoyansa da ke cike da sha’awar hakan cewa kasar Mexico za ta biya kudin gina katangar.
To saidai a tattaunawar da su ka yi ranar Talata, mutanen biyu sun yi muhawara kan wannan batu. Pena Nieto ya bukaci Shugaban na Amurka ya fito karara y ace kasar Mekziko ba za ta biya kudin gina katangar ba, to amma Trump ya ki.
Wani jami’in gwamnatin Mekziko ya ce Trump ya kuhula lokacin tattaunawa ta wayar, to amma wani jami’in gwamnatin Amurka ya karyata da cewa abin da ya faru kawai shi ne Trump ya yi takaicin hakan, a cewar jaridar.