A karo na bakwai tun bayan dawowar tsarin mulkin dimokuradiyya a Najeriya a shekarar 1999, tawagar kwamitin sa ido na zabe daga kungiyar kasashe rainon ingila wato Commonwealth a turance ta iso cikin birnin tarayya Abuja baya ga samun gayyata daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar wato INEC.
Tawagar kungiyar mai manufar yin bibiya ga yadda ake ci gaba da yin shirye-shiryen tunkarar zaben ranar Asabar mai zuwa da kuma sanya ido a kan yadda zaben zai gudana ta sami jagorancin tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Thabo Mbeki, wanda ya ce aikinsu a matsayin tawaga shi ne sanya ido da kuma tantance yanayin da shirye-shiryen zaben ke ci gaba da kankama, sanya ido a kan ayyuka a ranar zabe, da kuma bayan zabe ta yadda zasu yi la'akari da duk abubuwan da suka shafi sahihancin tsarin zabe wanda ya yi daidai da ainhin yanayin da ya kamata a gudanar da zabe a karkashin tsarin mulkin dimokaraddiya tsari da ita kanta Najeriya ta amince da shi.
A cewar Thabo Mbeki, tawagar dai ta iso birnin tarayyar Najeriya ne a ranar 18 ga watan Febrairun da muke ciki domin tabbatar da sauke nauyin aikin da ya rataya a wuyanta inda jagora Mbeki ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a harkar zaben da su mutunta alkawurran da suka dauka na tabbatar da cewa an yi zabe cikin zaman lafiya da lumana.
A kan batun zaben na ranar Asabar, Mal. Garba Abari wanda shi ne babban daraktan hukumar wayar da kan al’umma ta Najeriya wato NOA, ya bayyana cewa hukumarsa ta yi ta aika sakonni a gidajen rediyo, kasidu da aka fassara a harsuna 33 da sauran kafaffen yadda labarai ga ‘yan kasa don fadakarwa a kan zaben dake tafe.
A wani bangare kuma, Mal. Garba Abari ya yi jan hankali ga ‘yan kasa a game da illolin sayar da kuri’unsu yana mai cewa hakan ba zai haifar da da mai ido ba.
Kasancewar a kusan karshen watan Maris zuwa farko-farkon watan Afrilun ne za’a gudanar da aikin kidayar al’umma a Najeriya, Mal. Abari ya bayyana mahimmancin aikin da za’a yi ta yadda gwamnati zata iya samar wa ‘yan kasa ababen more rayuwa da kuma kawar da matsalolin tsaro a kasar.
Kazalika, bayan zaben na ranar Asabar, tawagar sa ido na Commonwealth, zata gudanar da taron manema labarai a birnin Abuja don sanar da sakamakon farko na aikin sanya ido a zaben da aka kamalla sa’anan ta koma mazauninta kafin ta fitar da cikakken rahoto da shawarwarinta a kan yadda zaben Najeriya ya gudana don mikawa babban sakataren kungiyar Commonwealth, sai gwamnatin Najeriya, hukumar INEC, shuwagabannin jam’iyyun da suka shiga zaben, tare da shuagabannin kasashen rainon Ingila kafin nan a fitar da shi don amfani ga kowa a duniya.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5