Shugaban Majalisar Ministocin Italiya Ya Kai Ziyara Nijar

Fraministan Italiya Giuseppe Conte da shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamdou Issouhou

Shugaban majalisar ministocin Italiya ya gudanar da ziyarar aiki ta wuni guda a jiya talata a jamhuriyar Nijer inda suka tantauna akan wadansu mahiman batutuwa

A jawabinsu na hadin guiwa ga manema labarai, yayin ziyarar ta farko tun bayan da kasashen biyu suka bude sabon babin huldar diflomasiya, Shugaban gwamnatin Italiya Giuseppe Conte da mai masaukin baki Mahamdou Issouhou na Nijer, sun bayyana ci gaban da ake samu a yunkurin kasashen biyu na yaki da ta’addanci da yaki da kwararar bakin haure, da safarar makamai, da kuma miyagun kwayoyi.

A nashi bayanin, Shugaban kasar Nijar ya bayyana gamsuwa da gudunmuwar Italiya wajen samun nasarorin wannan yaki ya kuma ce, muddin ana son cimma gurin da aka sa gaba akan maganar yaki da kwararar bakin haure zuwa Turai, dole ne a taimakawa Afirka fita daga kangin talauci, ya kuma zama wajibi kasashen yammaci su daina daukar nafiyar a matsayin wani rumbun dibar ma’adanan karkashin kasa.

Shugaban gwamnatin ta Italiya ya ci alwashin ci gaba da tallafawa Jamhuriyar Nijar wacce ya ce tana da matukar mahimmanci wajen tabbatar da tsaro a kasashen yankin Sahel da yankunan arewaci da gabashin Afirka har ma da nafiyar Turai kanta.

A karshen wannan ziyara, Shugaban gwamnatin Italiya Giuseppe Conte, ya ziyarci ofishin hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan ci rani IOM kafin daga bisani ya je ofishin hukumar UNHCR mai kula da ‘yan gudun hijira domin jinjinawa kokarin da jami’ai a wadanan fannoni suke yi.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Ziyarar Fraministan Italiya a Nijar-3:00"