Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Aikin Gina Wasu Manyan Hanyoyi a Jamhuriyar Nijar


Bikin kaddamar da aikin gina hanya a Nijar
Bikin kaddamar da aikin gina hanya a Nijar

Shugaban kasar jamhuriyar Nijar Mahamadu Isufu, ya kaddamar da fara aikin shinfida kwalta, daga Damagaram zuwa Tanut mai tsawon kilomita 138. Hanyar ta hada kasashen kudu da sahara tun daga Nijeriya har zuwa Algeria.

A lokacin da ya kaddamar shugaban kasa ya ce hanyar na da muhimmanci idan aka yi la'akari da yadda za ta habaka huldar kasuwanci tsakanin kasashen, inda ya ci gaba da cewa tuni an fara aikin hanyar Arlit zuwa Algeria, Mahamadu Isufu ya ce hakan zai maido ma Damagaram matsayin ta na tarihi, wato cibiyar cinikayya .

Haka ma babban al'amari ne ga Damagarawa musamman matasa, za su samu aikin yi, kuma wani ci gaba ne ga tattalin arziki, ya kuma ci gaba da cewa wannan aiki Tarayyar Turai ce ta tallafa wa Nijar.

Bikin kaddamar da aikin gina hanya a Nijar
Bikin kaddamar da aikin gina hanya a Nijar

Dakta Denise Elena Iyonete, wakiliyar Tarayyar Turai ta ce wannan aiki na da muhimmancin gaske ga jamhuriyar Nijar, domin zai saukaka al'amarin kasuwanci da hulda tsakanin al’umomin kasashe shida, na adadin ‘yan Afirka dubu dari hudu, haka kuma dama ce ta yin musayar kayayakin kasuwanci ta hanyar cinikayya a nahiyar Afirka.

Domin karin bayani saurari rahotan Tamar Abari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG