“Ba zan kara zama da wannan mutumin ba, saboda irin abubuwa da ya yi a baya da suke nuna ba zai yiwu a kulla wani hadin gwiwa da shi a siyasance ba”, inji Firai minister Fayez al-Serraj yana fadawa Reuters.
Sojoji masu biyayya ga al-Serraj da masu biyayya ga Janar Khalifa Haftar sun yita yaki a wajen birnin Tripoli da zummar karban ikon babban birnin, lamarin da yayi sanadiyar arcewar dubban fararen hula zuwa cikin birnin domin kubutar da rayukarsu.
Al-Serraj yace ganawar su da Haftar ta karshe a cikin watan Faburairu tamkar wata dama ce da ya samu domin kara shiri ya aika da jiragensa su kai farmaki da bama bamai a kan Tripoli.
Babbar manufar ayyukan mu na soja itace kare Tripoli, inji Al-Serraj, ya kuma yi alkawari cewa za a ji labari mai dadi a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.