Sakatariyar Yada Labaran Fadar White House Sarah Sanders, ta gaya ma manema labarai cewa wasikar, a ta bakinta, "na cike da lafazi da kuma manufa mai kyau." Sarah ta yi nuni da wasikar a matsayin shaidar cewa ana samun cigaba a huldar Amurka da Koriya Ta Arewa a tattaunawar da ake yi ta kau da makamin nukiliya a yankin ruwan Koriya.
Ta kafar twitter, a ranar Lahadi, Trump ya yaba da irin faretin da aka yi a Koriya Ta Arewa wanda bai hada da baje kolin makaman masu linzami ba.
To amma sabanin yadda fadar White House ke ganin al'amarin, da dama daga cikin masu lura da al'amuran yau da kullum na ganin dangantaka ta dan yi tsami tsakanin kasashen biyu. Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya dakatar da shirinsa na kai ziyara Koriya Ta Arewa a watan jiya bayan cijewar tattaunawar da kasashen ke yi.