Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro yana neman wa’adin mulki na biyu na shekaru shida a zaben da aka gudanar yau lahadi da ‘yan hamayya suka kauracewa da cewa, dauki dora ne za a yiwa dan mulkin kama karya, al’ummar kasa da kasa kuma suka yi Allah wadai da zaben.
WASHINGTON, DC —
Ana kyautata zaton, Maduro, dan shekaru hamsin da biyar, tsohon direban motar safa,zai lashe zaben duk da rikicin da ake fama dashi da ya haifar da karancin abinci da tashin gwauron zabon farashin kayayyakin masarufi, yayinda ayyukan hakar mai a kasar yayi kasa a kasar da ta kasance daya daga cikin kasashen da suka fi sayar da mai a kasasahen duniya.
Tsohon gwamnan jiha Henri Falcon shine baban mai kalubalantar Maduro sai dai fitowar wani dan takara na biyu, Pastor Javier Bertucci, dake kalubalantar Maduro zata rage mashi tasiri a takarar.
Nasarar Maduro a zaben zata sa a kara kabawa kasar sabbin takunkumi da suka hada da takunkumin albarkatun mai daga gwamnatin Amurka da kuma Kungiyar Tarayyar Turai da kasashen kudancin Amurka.