Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Ta Kange 'Yan Adawa Daga Takarar Shugabancin Venezuela


Shugaban Kasar Venezuela Nicholas Maduro
Shugaban Kasar Venezuela Nicholas Maduro

Hukuncin kotun koli a Venezuela ya bar 'yan adawa da jimamin ta yadda za su bullowa hukuncin da aka yanke na kare 'yan adawa daga kwamawa da shugaba Nicolas Maduro a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Babbar kotu a Venezuela ta fitar da hadakar 'yan Adawa daga Zaben shugabancin kasa da ke karatowa, wani yunkuri da yake nuni da Shugaba Nicolas Maduro mai sassaucin ra’ayi kuma mara farin jini zai yi nasara.

An shirya fara rijistar jam’iyyu da 'yan takarar da zasu tsaya takarar zaben a karshen makon nan. Duk da haka babbar kotun kolin kasar ta fadawa hukumar zabe ta kasa da ta dakatar da Yin Rigistar a ranar Alhamis har sai bayan watanni shida.

Kotun bata bada wani kwakkwaran dalili na wannan hukuncin da ta yanke ba. Za’a gudanar da zaben shugaban kasar ne a karshen watan Afrilun shekarar nan ta 2018, wanda zai bar 'yan adawa da kasa tsaida 'yan takararsu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG