Tsohon jagorar ‘yan adawa na kasar Venezuela Antonio Ledezma ya isa Madrid yau asabar inda ‘yan uwansa suka yi masa marhabin lale da zuwa.
Ledezma yace wanene yace kasar Venezuela bata cikin damuwa, to ba shakka tana cikin damuwa domin ko abinda ya tafi ya tattauna Kenan da prime ministan kasar Spain Rajoy
Ledezma wanda akayi wa dauri talala tun a shekarar 2015 ana tuhumar sa da yunkurin juyin mulki, yace ya gudu daga wannan daurin talalan a ranar jumaa inda ya tafi makwabciyar kasar wato Colombia, inda ya yace ya gitta shingen yan sanda dasojoji da dama.
Sai dai kafin ya bar Colombia,Ledezma yace yana shirin yaki ne da neman yancin samar da demokaradiyya mai yanci a kasar su ta Venezuela.
Ladezma wanda tsohon magaji garin Caracas ne, yace tuni yayi Magana ta wayan tarho da shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos wanda ya nuna zai goya wa wannan yunkuri nasa baya.
Suko a wuri daya jamia’an shige da fice na kasar Colombia cewa suka yi Ledezma ya shiga Colombia ne ta hanyar data dace bayan ya gitta gadar SIMON BOLIVAR wadda ta raba kasashen biyu.
Sai dai shugaban kasar Venezuela Nicholas Muduro yace yana sane da gudun Ledezma wanda yakan rika yiwa zunde yana kiran sa fatalwa.
Maduro yace mutanen Madrid suyi hankali da wannan mutumin.
Shi dai Ledezma dan shekaru 62 da haihuwa ya jagoranci zanga-zanga a shekarar 2014 domin sukan lamirin gwamnatin Muduro abinda ya haifar da tashin hankali a kasar wannan yasa aka daure shi gidan yari har na tsawon wasu watanni, kafin daga baya a mayar da shi daurin talala saboda da dalilan rashin lafiya.
Facebook Forum