Shugaban Kasar Najeriya Zai Kai Ziyara Jihar Neja

Shugaba Goodluck Jonathan

Ganin yadda zaben shekara mai zuwa ke karatowa shugaban Najeriya zai kai ziyara jihar Neja wadda a da gwamnata ya buturewa shugaban
A karon farko tun lokacin da wasu gwamnoni suka yiwa jam'iyyar PDP tawaye har da shi ma gwamnan jihar Neja sai gashi shugaban, Goodluck Jonathan, zai kai ziyara.

Gobe Asabar ake sa ran shugaban kasa zai isa jihar Neja domin soma wata ziyara. Yayin ziyarar zai halarci taron gwamnoni takwas dake tsakiyar kasar da za'a yi a Minna babban birnin jihar.

Gwamnan jihar Neja yace yana fata ziyarar ta shugaban kasar zata sa a hanzarta kammala ayyukan da gwamnatin tarayya keyi a jihar . Farfasa Muhammed Kute Yahaya kwamishanan labarai na jihar Neja yace jihar na cikin jihohin da suka fi hanyoyin gwamnatin tarayya kuma yana fata za'a gyarasu.

Ita ma jam'iyyar PDP reshen jihar tace duk da cewa tana da karfi a jihar amma ziyarar shugaban tamkar kara mata karfin gwiwa ne kamar yadda Alhaji Hassan Saba jami'in labaran jam'iyyar ya fada. Ya kira 'yan jarida su fadawa duniya yadda jam'iyyar ke da karfi a jihar Neja. Yadda zasu karbi shugaban kasa zai nunawa jama'a irin tagomashin da jam'iyyar ke dashi a jihar. Yace duk wanda ya cancanta ya kasance a wurin tarbar shugaban za'a ganshi.

Amma Sanata Ibrahim Musa shugaban riko na jam'iyyar APC a jihar yace da zuwan shugaban da ma rashin zuwansa bai canza komi ba domin PDP dama ba cin zabe takeyi ba. Yace idan za'a yi zabe ba tare da satar akwati ba babu yadda za'a yi PDP ta ci zabe a jihar Neja.

Ga rahoton Mutapha Nasiru Batsari

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Kasar Najeriya Zai Kai Ziyara Jihar Neja-2' 27"