Shugaban yayi furucin ne a birnin Ilorin fadar gwamnatin jihar a wurin bikin karbar manyan mutanen jihar cikin jam'iyyar ta PDP. Shugaban ya godewa jama'ar Kwara da irin gagarumar maraba da suka yi masa. Yace babu shakka muanen jihar suna tare da jam'iyyarsu da abubuwan da suke yi. Yace a jam'iyyar PDP ko mene addinin mutum ko kabilarsa yana yin abun da ya ga dama ba tare da wata tsangwama ba.
A cigaba da jawabinsa shugaban ya bukaci 'yan siyasa su rika yin la'akari da bukatun jama'a. Shi ma mataimakin shugaban Alhaji Namadi Sambo yace ayyukan gwamnatin tarayya suna tasiri a jihar. Yace irin tarbar da aka yi masu manuniya ce ayyukansu na tasiri a jihar wadannan suka hada da ilimi, da aikin gona da gyara filin jirgin sama.
Shugaban majalisar dattijan Najeriya dake cikin tawagar David Mark yace abun da suka gani ya nuna karara cewa jihar Kwara jihar PDP ce. Taron na yini daya ya samu halartar jigajigan shugaban jam'iyyar PDP ciki har da shugaban jam'iyyar na kasa Alhaji Adamu Muazu da shugaban kwamitin amintattu na kasa Tony Anenih.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal