Shugaban Kasar Najeriya Kan Sakin ‘Yan Makaranta Da Aka Sace

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Juma'a ya ce gwamnati za ta "ci gaba da kokarin" kare daliban makaranta a cikin kasar bayan da wadanda suka yi garkuwa da sama da dalibai 300 suka sake su.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Juma'a ya ce gwamnati za ta "ci gaba da kokarin" kare daliban makaranta a cikin kasar bayan da wadanda suka yi garkuwa da sama da dalibai 300 suka sake su.

An sace yaran ne a daren 11 ga Disamba daga makarantar Sakandiren Kimiyya ta Gwamnati, ta maza zala da ke kauyen Kankara a cikin jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce.....

"Mun gode Allah, da kuma Kungiyoyin ‘Yan Sanda da musamman kungiyar sojoji da kuma gwamnann da ya nuna kwazo game da wannan aikin. Gwamnan ne ya kira ni ya sanar da ni, na kuma yi mashi barka da shi da sojojin sabili da irin hadin gwuwar aikin mai kyau da suka gudanar.

Ban gamsu da aikin su ba, su ya kamata su tabbatar da tsaron jama’a kasar, da ayyukan kasar amma ba su yi haka ba,

Muna iyakacin kokarinmu. Idan za a tuna mun rufe iyakokinmu amma sai muka ga cewa ‘Yan ta’addan ko masu satar mutane basu daina samun bindigogi ba, har yanzu suna kama mutane don neman kudin fansa suna karban miliyoyin naira, muna da aiki mai yawa nan gaba.”

Karin bayani akan: Boko Haram, sojoji, Buhari, Kankara, da jihar Katsina.