Rahotanni da dama sun ruwaito rundunar sojin kasar Chadi na cewa shugaban Idriss Deby Itno ya rasu.
Bayanai sun yi nuni da cewa shugaban ya mutu ne a filin daga inda dakarun kasar ke fafatawa da ‘yan tawaye a cedar kamfanin dillancin labarai na AP.
Shugaba Deby wanda ya mulki kasar ta tsakiyar Afirka sama da shekaru talatin, ya mutu ne a ranar Talata, babban kwamandan sojojin kasar ya sanar a gidan talabijin da rediyo na kasar.
Wannan sanarwa mai ban mamaki ta zo ne sa’o’i kadan bayan da jami’an zaben suka bayyana Deby a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar na ranar 11 ga Afrilu, wanda hakan ya ba shi damar ci gaba da kasancewa kan karagar mulki na karin shekara shida.
Karin bayani akan: Idriss Deby, Boko Haram, kasar ta Chadi, da Chad.
A ranar Litinin gangamin yakin neman zabensa ya bayyana cewa shugaban zai ziyarci dakarun kasar da ke fada da ‘yan tawaye, wandanda suka tunkari birnin N’Damena daga kan iyakar kasar Libya a cewar Reuters.
Dan shekara 68, Idriss Deby ya hau karagar mulki ne a shekartar 1990, yana kuma daya daga cikin shugabannin Afirka da suka dade akan karagar mulki.
Kasashen yammaci na kallon Deby a matsayin abokin tafiya a yaki da duniya ke yi da mayaka masu ikrarin jihadi, irinsu Boko Haram a yankin Tafkin Chadi da kuma kungiyoyi da ke da alaka da Al Qaeda da IS a yankin Sahel.
Ya zuwa yanzu, ba a san takamaiman yadda shugaban ya mutu ba.
Sabon Shugaban Mulkin Sojin Chadi A Wajen Jana’izar Mahaifinsa
Your browser doesn’t support HTML5
An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
Your browser doesn’t support HTML5