Gwamnan wanda yake jawabi a wani babban taron kasa da kungiyar zumunta zabi sonka ta gudanar a Minna yace yanzu lokaci yayi da 'yan arewacin Najeriya zasu hada hannun domin ceto yankin daga bala'in da ta abka.
Gwamnan yace idan ma akwai masu tausayin 'yan Boko Haram to su daina tausayinsu domin kome suka saki zai iya nuna banbancin musulmi da wanda ba muslmi ba. Ya roka da sunan Allah a taimakawa yankin domin jama'a da yawa basa zama lafiya saboda nuna banbanci da kuma jahilci. Idan ba jahili ba wanda Allahnsa yace babu tilastawa a batun shiga addini kana kai ka ce zaka kashe mutane idan basu shiga addininka ba. Shin yaya zaka kashe mutane su kuma shiga addininka. Kai kanka ba tilasta maka aka yi ba. Kila an haifeka ne a addinin. Baka san komi ba sai neman shugabanci na karfi da yaji.
Shi kuma sabon shugaban kungiyar zumunta zabi sonka a Najeriya Umaru Jirgi Mai Hoto Wamako yace kiran da gwamna Babangida Aliyu yayi yana da matukar mahimmanci saboda haka zasu bada hadin kai dari bisa dari. Kungiyarsu ta kasa a shirye take ta bada hadin kai domin babu yadda za'a yi su cigaba da kallo kawai ba tare da tashi su yi wani abu ba. Dole su tashi tsaye su yaki ta'adancin da Boko Haram ta ke yiwa arewa.
Na farko zasu yaki ta'adanci da rokon Allah ba dare ba rana. Nabiyu suna da matasa da zasu bi hanyoyi na asiri su shawo kan lamarin.
Kungiyar kare hakin bil Adama dai tace rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabas yayi sanadiyar hallaka mutane dubu goma. Kawo yanzu ita kungiyar ta Boko Haram tana rike da 'yan mata sama da dari biyu da suka sace a wata makaranta dake jihar Borno. A halin yanzu ma rahotanni daga jihohin Borno da Yobe na nuna kungiyar ta Boko Haram na rike da ikon wasu garuruwa a ciki har da Liman Kara a jihar Borno inda akwai wata kwalajin horas da 'yansanda.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5