Laftana kanal Paul Henri sandaogo Damiba wanda ya yi shigar tufafin farar hula ya je Nijer ne domin tantauna hanyoyin da za a bullowa matsalar tsaron da ta ki ta ki cinyewa a yankin da ‘yan ta’adda ke ci gaba da karkashe dimbin mutane tare da tilasta wa dubbai tserewa daga matsugununansu ba’idin koma bayan tattalin arziki da tsayawar harakoki da dama.
Kamar sauran kasashen G5 Sahel Burkina Faso na fama da hare haren ‘yan ta’addan yankin sahel abinda ya sa masu sharhi akan al’amuran yau da kullum ke kallon wannan ziyara da mahimmanci.
A takaitacen bayanin da ya yi wa manema labarai jim kadan bayan ganawarsa da shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum, shugaban gwamnatin mulkin sojan ta Burkina faso yace "kun san matsalolin tsaro akan iyakokin nan 3 abu ne da ke matukar tada hankali shine makasudun wannan ziyara da na kawo wa shugaban kasar Nijer domin mu yi nazari akan kalubalen da muke fuskanta akan iyakokinmu don ganin mun zakulo hanyoyin da muka tunkari wannan al’amari."
Kafin wannan rangadi na birnin Yamai shugaban gwamnatin rikon kwaryar Burkina Faso laftana kanal Paul Henri Sandaogo Damiba ya ziyarci kasashen Mali da Cote d’ivoire a makon jiya inda suka tantauna akan batutuwan da suka shafi sha’anin tsaro da a daya gefe, dambarwar da ke tsakanin wadanan kasashe bayan da gwamnatin kanal Asimi Goita ta cafke sojoji 49 na Cote d’ivoire da tace sun shigo Mali ba akan ka’ida ba wadanda kuma take kallonsu a matsayin sojan haya a wani lokacin da ake ta neman hanyoyin bikon kasar ta Mali wace ta bada sanarwar ficewa daga kungiyar G5 SAHEL a watan afrilun da ya gabata.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5