Cazeneuve zai maye gurbin Manuel Valls, wanda yayi murabus yau Talata don neman tsayawa takarar zaben shugaban kasa da za a yi shekara mai zuwa, karkashin jam’iyyar Socialist Party. Valls dan shekaru 54 da haihuwa ya jefa sunansa cikin masu neman maye gurbin shugaba Hollande, wanda ya sanar cikin makon da ya gabata a wata hira da aka yi da shi a kafar talabijin, cewa ba zai nemi tazarce ba.
A matsayin ministan harkokin cikin gida Cazeneuve na kan gaba wajen daukar mataki akan jerin hare-haren da ‘yan ta’adda da suka kai a kasar, wanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 200 cikin shekaru 2 da suka gabata, ciki har da hare-haren da aka kai a lokaci guda cikin shekarar da ta gabata a Paris wadanda suka kashe mutane 130.
Idan Valls ya sami nasarar zaben fidda gwanin jam’iyyar ta Socialist, zai kara da Francoise Fillon, dan shekaru 62 da haihuwa, tsohon firayin minista, wanda ya sami nasarar zama dan takarar jam’iyyar Center Right Republican party a cikin makon da ya gabata.