Firayin ministan na Japan zai kai ziyarar ce don nuna kudurinsa na hangen nan gaba da kuma tabbatar da ganin bala’in yakin duniya da aka yi a baya bai sake faruwa ba, ya kuma tura sakon neman sulhu tsakanin Amurka da Japan, a cewar sakataren majalissar zartaswar Japan Yoshihide Suga, a yau Talata.
Cikin wannan shekarar za a cika shekaru 75 da kai harin da ya sa Amurka shiga cikin yakin duniya na 2.
Watanni 6 da suka gabata, shugaba Obama, ya zamo shugaban Amurka na farko dake kan mulki da ya kai ziyara zuwa wani wurin tunawa da wadanda suka mutu a birnin Hiroshima na Japan, inda a shekarar 1945 Amurka ta jefa bam din nukiliya na farko a duniya a karshen yakin da aka yi.
Mathew Linley, wani farfesa a jami’ar Nagoya, ya ce a ganin Abe da magoya bayansa dake Japan wannan ziyarar zata kawo karshen lokacin da ya biyo bayan yakin da aka yi.
A wani lamari na dabam kuma, Wani mai yiwa jam’iyyar Republican hidima a fannin manufofin hulda da kasashen waje ya isa kasar Taiwan a safiyar yau Talata a wata ziyara ta mako daya, wacce tayiwu ta hada da ganawa da shugaba Tsai Ing-wen, bayan da ta taya shugaba Donald Trump mai jiran gado murnar nasarar da ya samu ta wayar tarho ranar Jumma’ar da ta gabata.