Shugaban Faransa Ya Kira Majalisun Amurka Su Kare Yarjejeniyar Nukiliyar Iran

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayinda yake gaisawa da 'yan majalisun Amurka

A cikin jawabinsa da yayiwa majalisun Amurka shugaban Faransa ya soki manufofin shugaban Amurka tare da kiran 'yan majalisun su tabbatar Donald Trump bai yi watsi da yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka cimma ba

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kira ga yan majalisar dokokin Amurka da su tabbatar, Amurka bata yi watsi da yarjejeniyar nukiliyar Iran ba, da nufin hanata ci gaba da kera makaman nukiliya.


A cikin wani jawabin mai dimbin tasiri na mintuna 49 da ya yi ga majalisun Amurka, Macron yace Iran ba zata taba mallakar makaman nukiliya ba, nan da shekaru biyar ko kuma shekaru goma.

Sai dai shugaban na Faransa bai bayyana shugaban Amurka Donald Trump kai tsaye a matsayin mai kalaman adawa ga yarjejeniyar shekarar 2015 a kan canjin yanayi.


Trump yana da wata daya kacal ya yanke hukunci a kan ko Amurka zata sabonta takunkumi a kan Iran. Yarjejeniyar ta dage takunkumi a kan Tehran yayin da ita kuma zata dakatar da shirinta na nukiliyar zuwa wani wani lokaci.


A hahlin da ake ciki kuma shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel zata kawo ziyarar wuni guda zuwa fadar White House a gobe Juma’a, baya ziyarar wuni uku da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kawo. Ana kallon wadannan ziyarce ziyarce masu biye da juna a matsayin wani yunkurin rokon shugaban na Amurka Donald Trump, kada ya yi watsi da yarjejeniyar nukiliyar Iran kana kuma ya baiwa kasashen Turai rashin biyan kudi jadawali Amurka ta dorawa karafan da ake shigowa dasu a cikinta na din din din.