Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Faransa Sun Bukaci Fadada Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Iran


Shugaban Amurka Trump da Shugaban Faransa Macron
Shugaban Amurka Trump da Shugaban Faransa Macron

Yayinda suke ganawa a Fadar White House dake nan Amurka shugaban Amurka Donald Trump da na Faransa Emmanuel Macron sun bukaci a fadada yarjejeniyar da aka cimma da Iran ta hada da makamai masu linzami da kokarin da Iran ta keyi na kafa ikonta a Gabas ta Tsakiya

Shugabannin Amurka da Faransa, sun yi kira da a fadada matsayar da aka cimma da Iran, amma kuma yayin da suke magana da manema labarai a jiya Talata, shugaba Donald Trump, bai nuna wata alama da ta nuna cewa Amurka za ta janye daga matsayar da aka cimma da hukumomin Tehran ba, kan shirinsu na mallakar makamashin nukiliya.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya ce bai san matakin da Shugaba Trump zai dauka kan wannan matsaya ta hadin gwiwa ba, yana mai nuni da wa’adin da zai kare a wata mai zuwa kan sabunta matsayar cirewa Iran takunkumin da aka saka mata domin a ci gaba da raya matsayar hadin gwiwar da aka cimma, wacce ake kira Joint Comprehensive Plan of Action a turance ko kuma JCPOA a takaice.

ACT: “Ni da Emmanuel mun tattauna cewa ba za mu ba Iran wata damar yin walwala ba a yankin Medtareniya ba, musamman idan aka yi la’akkari da cewa mu ke da karfin fada a ji.”

A jiya Talata, shugaba Trump ya yi kakkausar suka akan wannan shiri, inda ya kwatantata shi a matsayin “hauka kuma abin dariya”, wanda tun asali bai kamata yi shi ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG