Shugaban kamfanin sada zumunci na Facebook Mark Zuckerberg na son kawar da kwayoyin cuta kafin karshen wannan ‘karni.
Hamshakin mai kudin kuma Biloniya da matarsa Priscilla Chan, sunce zasu bayar da Dalar Amurka Biliyan 3 cikin shekaru Goma masu zuwa domin bunkasa harkar binciken kawo karshen cututtuka.
Wani kaso mai tsoka na kudin, kimanin Dala Miliyan 600 za’a bada shi ne ga wasu manyan makrantun jami’oi guda biyu ne dake a jihar California da zasu gudanar da bincike kan yadda za’a ga karshen cututtukkan da aka auna.
A lokacin da take wani jawabi mai sosa rai a jami’ar UCSF, Chan tace “Mark da ni mun shafe shekaru biyu muna magana da masana kimiyya daga kan shahararru har zuwa ‘daliban jami’an da suka kamalla manyan digirorinsu akan wannan al’amari. Ms Chan ta ci gaba da cewa “Munyi imanin cewa duk irin rayuwar da muke son ‘ya ‘yan mu su samu, abu ne mai yiwuwa. Mun shatawa kanmu kuduri ne na cewa: shin zamu iya kawar da duk cututtuka a lokacin rayuwar ‘ya ‘yan mu? Kuma wannan ba yana nufin cewa ba babu wanda zai sake kamuwa da wata cuta ba. Amma yana nufin ‘ya ‘yan mu da jikokinmu ba zasu rinka kamuwa da cuta kamar yadda ake yi a yanzu ba, abin zai ragu matuka. Kuma zamu dauka cewa zamu samu hanyoyin sanin lokacin da cututukkan zasu diro akan mu, kuma mu iya sarrafa su ta yadda ba zasu wahalar ba. Ni da Mark Mun yarda da cewa wannan abu mai yiwuwa ne a rayuwar ‘ya’yanmu.”
Wata sannaniyar likita da ta kware akan fannin kiyon lafiya mai suna Cori Bargmann ce zata gudanarda wannan sabuwar cibiyar da ake magana a kanta.
Zuckerberg da Chan sun yi wannan sanarwa ne a jiya Laraba. A cewar Zuckerberg “Za’a ‘dauki shekaru kafin a kirkiri kayan aiki na farko, haka kuma zai sake ‘daukar wasu shekarun kafin a kawar da cutar farko. Dole ne mu zamanto masu hakuri.”
Mark Zuckerberg da uwar dakinsa suna daga cikin wani kulob na attajiran duniya masu son tallalafawa marasa galihu, shirin da a turance ake kira “Giving Pledge”, inda hamshakan masu kudi ke alkawarin bada rabin daukacin dukkan dukiyar da suka mallaka ga aiyukkan jin ‘kai. Sauran hamshakan attajiran dake cikin wannan Kulob sun hada da Bill da Melinda Gates. Da Warren Buffer da sauransu. Zuckerberg da matarsa sunyi alkwarin bayar da kaso 99 cikin 100 na dukiyarsu.
An kirkiri shafin Facebook a shekara ta 2004, kuma tun wancan lokaci kamfanin ya bunkasa sosai inda ya fitar da alkaluman kudin da ya samu a wattani ukku na karshen wannan shekara, wanda ya kai Dala Biliyan 4 da milyan dari 5. Kamfanin yace sama da mutane miliyan dubu 1 ne ke amfani da shafin Facebook a kullu yawmin, kuma sama da kashi 80 cikin 100 na su suna kasashen duniya ne yayinda sauran kashi 20 ne kawai ke Amurka da Canada.
Your browser doesn’t support HTML5