Masu iya magana dai kance, duk abun da yake da kyau, to yana da wahalar samu. Hukumar binciken sararrin samaniya NASA, na zagaye na karshe, wajen kokarin dawo da na’urar da suka aika cikin sararrin samaniya, don zurfafa bincike a sararrin.
Masanan dai sun bayyanar da cewar, duniyar wata na zagaye ne kamar zobe, inda suka lakama wannan binciken da suke gudanarwa da suna “F-Ring” suna tsammanin a karshen wannan shekarar zasu fitar da sakamakon binciken su, wanda suke sa ran wata zai kusanci duniya rana a dai-dai lokacin.
Jirgin na “Obiter” zai kusanci duniyar “Staturn” wanda yake shine watan da yafi kowanne girma. Anasa ran zaiyi tafiyar da ta kai kimanin kilomita dubu biyu da dari hudu 4,200, a tsakanin duniyar da wata.
Ana sa ran a ranar ashirin da bakwai na watan Afrilun shekara mai zuwa 2017 ne na’urar “Cassini” zata shiga wasu gurare da babu wani abu da ya taba shiga, a cikin sararrin samaniya. Wannan zata zama damar da zasuyi amfani da ita, da ba’a taba samu ba, wajen kusannatar duniyar wata.