Shugaban China Ya Ce Kofofin Kasuwancin China A Bude Suke

Shugaban China Xi Jinping

Masana na ganin muhimmin abu a jawabin shugaba Xi JInping a taron Boao ya bambance tsakanin salon kasuwancin Amurka da China

A lokacin wani babban taro na shugabannin kasashe, da ‘yan kasuwa da kuma masana a nahiyar Asiya da ma wasu nahiyoyin da ake kira Taron Boao, Shugaban kasar China Xi Jinping bai ambaci shugaban Amurka Donald Trump gaba-gadi ba akan rikicin cinikayya da ke cigaba da zafafa tsakanin kasar da Amurka.

To amma kudurorin da Xi ya dauka na yin garambawul a fannin tattalin arziki na da nasaba sosai da takaddamar cinakayya da kuma barazanar da shugaba Trump yayi ta sanya haraji mai yawa akan kayayyakin China da ake shigowa da su Amurka.

A jawabin da ya yi, Xi ya ambaci “budewa” har sau 42. Daya daga cikin batutuwa mafi muhimmanci a jawabin nasa shine “kofofin kasuwancin China na bude.” A cewar wani mai fashin baki, bayanin wani yunkuri ne na jaddada bambancin dake tsakanin salon China da Amurka.