A jiya Talata, Shugaban kasar Chadi Idriss Deby yace zai tsaya takarar shugabancin kasar karo na 5 a zaben da ke tafe a watan Afrilun shekarar nan, inda yayi alkawarin dawo da iyakar wa’adin mulki matukar ya ci zaben.
WASHINGTON, DC —
Mr. Deby dai ya kwace mulkin kasar ne ta juyin mulkin soji a shekarar 1990. An kuma dakatar da maganar wa’adin mulki ne a shekarar 2005 a lokacin da fadan addinin ya barke tsakanin Musulmai da Kiritocin kasar.
Shugaban yace, “ya zama wajibi mu sake dawo da wa’adin mulkin shugabancin kasa a cikin kundin tsarin mulkinmu, domin kuwa mun wuce lokacin da za a ce canza Shugaban kasa yana zama wahala”.
Ya kara da cewa, rayuwar kasar ta Chadi na fuskantar barazana tun lokacin da aka dakatar da wa’adin mulkin shugaban kasa a shekarar ta 2005. Chadi ta zama daya daga cikin manyan kawayen makwabtanta wajen yakar ta’addancin ‘yan Boko Haram din makwabciyarta Najeriya.