Shugaban Amurka Donald Trump Ya Yi Amai Ya Lashe

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake fitowa yana kare kansa da kuma ganawar sa da shugaban Rasha Vladmir Putin, kwana daya bayan ya sauya maganar sa ta amincewa da 'kin yardar da Putin cewa kasarsa tayi katsalandan a zaben shugaban kasar Amurka na 2016.

A safiyar yau Laraba Trump ya rubuta a shafinsa na twitter cewa: “Manyan jami’an binciken leken asiri na duka bangarorin magoya baya da masu adawa sun ji dadin bayanin da na gabatar a lokacin taron manema labarai a Helsinki. Ni da Putin mu tattauna kan abubuwa da dama masu muhimmanci a ganawar ta farko. Mun samu jituwa wanda ya dami yan bakin ciki dake son ganin mun yi fada. Manyan sakamako na nan tafe.”

Sakon da Trump ya rubuta a shafinsa na twitter ya biyo ne bayanda ya amsa cewa ya amince da matsayin da hukumomin leken asiri suka bada na cewa Rasha tayi kasalandan a zaben shugaban kasa na 2016.

Trump ya gayawa manema labarai cewa shima ya amince da cewa Rasha ta yi shisshigi a zaben shugaban kasa na 2016, amma ya kara da cewa ta yiwu akwai wasu mutanen da su ma suka taka rawa wajen yin katsalandan din.