Yace yana da kyau idan aka samu jituwa da Rasha mai makon akasin haka. Idan Rasha ta taimake mu a yaki da kungiyar ISIS, wadda babban yaki ne da masu ta'addanci da sunan addinin Islama a duk fadin duniya, hakan zai yi kyau, Mr. Trump ya gayawa tashar talabijin ta FOX a tattaunawa da suka yi kamin a fara gasar cin kofin kwallon zari-ka ruga na Amurka da ake kira Super Bowl da aka yi jiya Lahadi. "zan jitu da shi? bani da masaniya" inji Trump.
Da aka tambyeshi kan munanan abubuwan da Putin yayi a baya, kuma ta yaya Trump zai kalle shi da kima sanin tarihin abubuwa da yayi, Trump sai ya kwatanta Rasha da Amurka.
Yace "akwai nakasa da ya wa. Muma muna da makasa. Me kake tsammani? Kasar mu bata da laifi? Trump ya fada.
Da yake bada amsa cikin wanin shirin talabijin a tashar CNN, shugaban masu rinjaye a majalisar dattijan Amurka Mitch McConnell, yace baya jin "za'a iya gwada Putin na Rasha da Amurka.