A jajiberen taron kungiyar kasashe 7 masu karfin masa'anatu da ake kira G7 a takaice, shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki mai masaukin baki Firayi Ministan PM, Canada Justin Trudeau, har fadar White ta bada sanarwar cewa Mr. Trump zai kauracewa wasu zaman shawarwarin.
A sakonni da ya aike ta Twitter a maraicen jiya Alhamis, Mr. Trump ya soki PM Trudeau da kuma shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, akan dorawa Amurka dumbin haraji kan kayayyakinta da kuma kafa mata wasu shingaye.
Shugaba Trump ya ce PM Trudeau ya fusata ne kan batun yarjejeniyar cinikayya da Amurka da ake kira NAFTA a takaice.
Shugaban na Amurka ya hau Twitter ne bayanda PM Trudeau ya yi barzanar cewa sauran kasashen zasu ware Amurka daga jawabin bayan taro.
Shi ma a nasa sakon ta Twitter, shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya ce yayinda "Amurka bata damu ba idan aka maida ita saniyar ware,sauran shugabannin shida ba zasu damu ba, idan suka sanya hannu kan yarjejeniyar ba tare da Amurka ba.