Shugaban Amurka Na Da Bayanai Kan Shishshigin Rasha A Zaben 2016

Wani rohoto da jaridar New York Times ta fidda jiya Laraba ya bayana irin tarin bayanan da shugaban Amurka Donald Trump, ya samu akan rawar da shugaban Rasha Vladmir Putin ya taka a zaben shugaban kasar Amurka na 2016.

Wani rahoto rohoton ya yi karin haske kan kokarin da shugaba Donald Trump, ya sha yi na jingine zancen rawar da Rasha ta taka a galabar da ya samu kan yar takarar shugaban kasa ta jam’iyyar democrat, Hillary Clinton, ciki har da bayanan da ya yi ta yi, wanda a baya ya karyata, daga nan kuma ya zo ya yarda, da binciken da hukumar leken sirrin kasar ta yi tun bayan ganawarsa da Putin a Helsinki ranar litinin.

Fadar White House ta sami kanta cikin rudani kan ko shugaban ya karyata bayanan binciken da hukumar leken asirin Amurka ta yi.

A lokacin ganawar sa da majalisar zartarwar fadar White House jiya, da aka tambayi Trump, kan cewa shin ko Rasha na barazana ga Amurka, har yanzu ‘’ Shugaban sai ya girgiza kansa yace A’A na gode kwarai da gaske’’.