Shugaban Amurka Mai Jiran Gado Ya Fara Sauya Matsayinsa

Donald Trump sabon shugaban Amurka mai jiran gado

Akwai alamar cewa sabon shugaban Amurka dake jiran gado Donald Trump yana ta kara janye jikinsa daga wasu daga cikin alkawurran da ya dauka a lokacin yakin neman zaben da yayi – ciki harda alwashin da ya dauka na cewa zai jefa abokiyar takarar tashi Hilary Clinton a kurkuku.

A lokkacin ganawar da yayi da manyan editocin kafofin watsa labarai da dama ya sha saka kafarwando daya da su, ciki har da New York Times wacce ya sha la’anta, nan ma Trump ya chanja matsayinsa, inda yace yanzu yana mutuntua NY Times din, kuma ma yana karanta ta.

A wajen wannan haduwar ce yake nunawa kafofin watsa labaran cewa yanzu baya da wata niyyar neman a gudanarda wani bincike kan anfani da hanyar sadarwar kanta da Hilary Clinton tayi anfani da ita wajen aika sakkonin email a lokacinda take rike da mukamin SHWA, balle kuma maganar gidauniyar Clinton ta bada tallafi. Trump yace Hilary ta ji jiki matuka, ita da iyalinta sun sha bakar wahala a lokacin yakin neman zaben da ya bayyana a matsayin “mai wahala matuka.”

Tsohon M/garin New York, Rudy Giuliani, daya daga cikin manyan mukarabban Donald Trump wanda ma ha rake sa ran cewa za’a bashi wani babban mukami a sabuwar gwamnatin, yace kudurin Trump din daidai yake da abinda aka saba gani a siyasar Amurka:

Giuliani yace: “Abinda aka saba ne na al’adar siyasar Amurka, cewa in kayi galaba a zabe, sai ka manta wasu abubuwa, saboda haka in abinda Trump ya yanke shawaran yi ke nan, wannan daidai yake da abinda tarihin siyasa ya gada ke nan a Amurka.”

Ita ma maganar chanji da dumamar yanayi, wacce a lokacin kyampen, Trump yace kire-kiren China ne, yanzu ya chanja matsayinsa a kanta; a maimakon adawa, Trump yace ya fasa janye Amurka daga cikin Yarjejeniyar Kiyaye Yanayi ta Paris.