Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Shugaban Amurka Ya Fara Zaban Mutanen da Zai Yi Aikai Dasu


Sabon Shugaban Amurka Donald Trump dake jiran gado
Sabon Shugaban Amurka Donald Trump dake jiran gado

A wata sanarwa da ya fitar jiya Donald Trump ya nada shugaban jam'iyyarsa a matasyin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa kana ya nada wani fitaccen dan jarida a matsayin mai yi masa tsare-tsare da bada shawara

Reince Priebus shugaban jam'iyyar Republican wanda kuma ya tsaya kai da kafa yana goyon bayan dan takarar a lokacin da sauran shugabannin jam'iyyar suka guje masa, shi ne yanzu zai rike mukamin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ta White House.

Shi ko Steve Bannon wanda zai zama babban mai tsare-tsare da bada shawara shi ne ya shugabanci fafutikar neman zaben Donald Trump.

Baicin wadannan mutanen biyu Trump ya nada tsohon magajin garin birnin New York Rudy Giuliani a matsayin Antoni Janar din kasar. Kazalika ya nada Sanata Jeff Sessions a matsayin sakataren harkokin tsaro.

Shugaba Trump mai jiran gado yace zai kori mutane kimanin miliyan uku daga kasar wadanda aka samesu da aikata manyan laifuka irinsu fyade, kafa muggan kungiyoyi da safarar miyagun kwayoyi. Kana ya sake jaddada anniyar gina katanga tsakanin kasar Amurka da kasar Mexico.

Trump yayi kalamunsa ne yayinda ya tattauna da gidan talibijan din CBS a karon farko tunda aka zabeshi a wani shiri na 60 Minutes da aka san tashar dashi.

Dangane da sauran mutanen da basu da takardun zama amma basu aikata wani mugun laifi ba kuma suna taimakawa wurin habaka tattalin arzikin kasar Trump yace zai yi nazari a kansu bayan ya samar da tsaron duk iyakokin kasar.

To saidai har yanzu kasashen yammacin turai na cikin rashin sanin tabbas saboda basu taba tunanen Trump zai yi nasara ba. Yanzu sun sa ido su ga abun da zai yi da kawancen NATO inda Amurka ita ce babbar kawa mai ba kungiyar taimako mafi tsoka akan tsaron nahiyar Turai. Lokacin da yake fafutikar neman zabe ya sha alwashin duba kawancen da zummar rage kashe kudi a kai.

Kungiyar yammacin turai na ganin Mr. Trump a matsayin mutumin da bai san duniya ba ko manufofin diflomasiya dangane da harkokin duniya. Yanzu dai sai a sa ido a ga inda ya nufa.

XS
SM
MD
LG