"Za mu goyi bayanku dari-bisa-dari. Za mu kare masu kare mu kuma sam ba za mu taba yashe ku ba," a cewarsa.
A jawabin da ya yi bayan cin abinci da wasu sojojin da ake shirin tura su fagen daga, Trump ya bayyana cikakken goyon baya ga NATO, to amma sai ya ce, "Abin da kawai mu ke bukata shi ne dukkan kasashe mambobin NATO su rinka biyan kudaden da aka kasafta masu."
Ya kuma yi magana kan ISIS, wadda ya ce kungiya ce mai "aniyar kashe al'umma da dama" a fadin duniya. Ba tare da ambato umurninsa da ya rattaba hannu akai a makon jiya mai takaita shigowa Amurka ba, Trump ya ce ya dau mataki kuma zai cigaba da daukar matakin kakkabe abin da ya kira "tsattsauran ra'ayin addini" daga kasar.
Cibiyar sojin ta CENTCOM ce kan bayar da umurni da kuma taimakawa wajen gudanar da ayyukan soji da kawayen Amurka don tabbatar da matakan tsaro a yankunan Gabas Ta Tsakiya da Asiya.