Shugaba Trump Ya Yi Alwashin Samar Da Zaman Lafiya A Gasa Ta Tsakiya

Yau Talata Shugaban Amurka Donald Trump, ya sha alwashin yin duk abin da ya ke iyawa wajen kawo zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya, hurucin da ya yi kama da na Shugabannin Amurka, da su ka gabata, wadanda su ka yi wannan yinkurin amma su ka gaza.

Kokarin nasa na cimma zaman lafiya na zuwa ne a farko-farkon gwamnatinsa mai fama da dambarwar siyasar cikin gida, wadanda wasu daga cikinsu, Trump da kansa ne ya janyo su ta wajen irin kalamansa.

"Ina da sahihin fatan cewa Amurka, za ta iya taimakawa ma Isira'ila da Falasdinu su cimma zaman lafiya don su kawo cigaba ga yakin da mutanensa," a cewar Trump, bayan wata ganawa ta tsawon sa'a guda a birnin Baitalahmi da Shugaban Falasdinu Mahmud Abbas.

Trump, ya kara da cewa ya yi matukar imanin cewa, "Muddun Isira'ila da Falasdinu su ka cimma zaman lafiya, sannu a hankali hakan zai kawo zaman lafiya a daukacin Gabas Ta Tsakiya, kuma wannan zai kasance wani babban cigaba." a cewarsa.

Da ya ke jawabi ganga da Trump, Abbas ya ce babbar matsalar Falasdinawa ita ce mamaya da kuma gine-gine a yankunan Falasdinu da Isira'ilawa ke yi da kuma kin amincewa da kafa Falasdina da Isira'ila ke yi.