Yayin da lokaci ke karatowa na yiwuwar dakatar da ayyukan gwamnatin Amurka, shugaba Donald trump ya sanya hannu a kudurin kudi na dala triliyan 2.3 wanda ya kunshi dala biliyan 900 na tallafin coronavirus da kuma dala triliyan 1.4 na kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2021.
Shugaban ya kira kudurin kasafin kudin “abin kunya” bayan da ‘yan majalisar dokoki da na dattawa suka sanya mai hannu a makon da ya gabata, abinda ya sa suka kawo karshen watannin da suka kwashe suna zaman shawarwari da basu sa Trump ciki ba sosai.
Kin amincewar da shugaban ya yi ta ba mutane da yawa mamaki wadanda suka yi tunanin shugaban zai goyi bayan kudurin kudin, har sai da aka kwashe mako guda ‘yan Republican da ‘yan Democrat na yin kiran shugaban ya sanya hannu a kudurin.
Ba tare da sanya hannun Trump ba ko daukar matakin samar da kudaden na wani dan lokaci, ta yiwu a tsaida ayyukan gwamnati ranar Talata 29 ga watan Disamba. Da ma a jiya Lahadi wa’adin matakin da ke kare jama’a da basu biya haya ba daga kora da karin kudin tallafi ga wadanda suka rasa ayyukansu ya kare.