Shugaba Trump Ya Sallami Mukaddashiyar Attoni-Janar din Amurka

Shugaba Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya sallami mukaddashiyar atoni-janar din kasar Sally Yates don ta ki ta kare dokar hana shigowar wasu daga kasashe bakawi na musulmai saboda acewarta dokar ta saba ma kundun tsarin mulkin kasar Amurka

Nan da nan, Shugaban Amurka Donald Trump, da daren jiya Litini ya sallami mukaddashiyar Attoni-Janar din Amurka, wadda tun da rana ta bayar da umurni ga Ma'aikatar Shari'a cewa, kar ta kare umurnin Shugaban Kasa da Trump ya yi amfani da shi, wajen haramta shigowar mutane daga kasashe 7 masu yawan Musulmi, na wuccin gadi.

Wani bayanin Fadar Shugaban Amurka ta White House ya ce Mukaddashiyar Attoni-Janar Sally Yates, wadda a gwamnatin Obama aka nada ta, ta yi abin da ya kira, "cin amanar Ma'aikatar Harkokin Shari'a ta wajen kin aiwatar da umurnin da aka bayar don kare Amurkawa." Takardar bayanin ta kuma bayyana Yates "raguwa ce kan abin da ya shafi kan iyakar Amurka kuma raguwa kan batun shigowar bakin haure."

Takardar ta ce Trump ya tube ta ya maye gurbinta da Dana Boente, Attonin Gundumar Gabashin Virginia, a matsayin sabuwar mukaddashiyar Attoni-janar. Da alamar an kuma tantance mutumin da Trump ya zaba a matsayin wandan zai zama Attoni-Janar, wato Dan Majalisar Dattawa mai Wakiltar Alabama, Jeff Sessions.

Tunda farko a jiya Litini, Yates ta rubuta wasika ga lauyoyin Ma'aikatar Shari'a cewa, "nauyi ya rataya a wuyanta na tabbatar da cewa matsayinmu a kotu ya zo daidai da hurumin wannan ma'aikatar na tabbatar da adalci kullu yaumin da kuma kare duk abin da ke daidai."

Shugaba Obama ya nada Yates matsayin Mataimakiyar Attoni Janar a 2015, sannan gwamnatin Trump ta ce mata ta cigaba da rike mukamin har sai Majalisar Dattawa ta tabbatar da sabon attoni-janar.